Zaben 2019: Yemi Osinbajo ya sha kaye a rumfarsa

167

Jam’iyyar PDP ta lashe zaben shugaban kasa a rumfar mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo. Dan takarar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya samu yawan kuri’u 384, a rumfar dan takarar mataimakin shugaban kasar na jam’iyyar APC a Lagos. Osinbajo da ke takara da shugaba Buhari a jam’iyyar APC, sun samu yawan kuri’u ne 197. Mataimakin shugaban kasar ya sha kaye ne duk da ya bi layi tare da jama’a domin kada kuri’arsa.

Tun da safe Osinbajo ya kada kuri’arsa a rumfarsa da ke Victoria Garden City a Lagos. Mutane dai za su yi mamakin yadda mataimakin shugaban kasar ya gaza lashe rumfarsa ganin yadda ya bi gida-gida sako da lungu a yankin kudu maso yammaci yana yakin neman zabe.

Leave A Reply

Your email address will not be published.