Yan shekara 19 da 18 sun yanke kan dan shekara 10 a Legas

277

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas su cafke wasu matasa 2 da sabon gawar wani karamin yaro da suka yanke kansa a kan babban titin Ajah zuwa Epe.

Kakakin ‘yan sandan jihar Legas, CSP Chike Oti ne ya bayyana hakan a jiya Laraba, inda ya ce jami’ansu masu yaki da garkuwa da mutane ne suka cafke matasan a ranar Talatar da ta gabata da misalin karfe 8:30 na dare.

Kakakin ya ce, jami’an nasu sun yi kacibus da matasan biyu ne a yayin da suke gudanar da faturu a kan titin Ajah zuwa Epe, a layin Tunde Balogun da ke a unguwar Shapati, yankin Ibeju-Lekki, jihar Legas.

Matasan, wadanda ‘yan uwan juna ne da suka bayyana shekarunsu da 19 da 18, sun fadawa ‘yan sanda cewa wani ne me suna Sodiq Abefe ya basu kwangilar kawo kan mutum akan kudi N200,000.

Mun yaudari yaron ne ta hanyar aikensa ya sayo mana Coca-Cola, ko da ya dawo, sai muka shake shi muka yanke kansa da wuka,” inji wadanda suka aikata laifin.

Iyayen yaron da aka yankewa kan su shaida dansu mai suna Joseph Makinde mai shekaru 10 da haihuwa.

Zuwa yanzu dai ‘yan sanda sun bazama neman Sodiq Abefe, wanda shi ne ya bada kwangilar a samo masa kan mutum.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Imohimin Edgal ya mika kes din ga sashen bincike akan kisan kai da manyan laifuka don ci gaba da bincike

Leave A Reply

Your email address will not be published.