Videon Abun Kunya-Dan Fim Ya Kunyata Yar Uwarsa Yar Fim

244


DAN FIM YA KUNYATA ‘YAR FIM Daga:Maje El-Hajeej Hotoro A wani shiri da Aminu Shariff da aka fi sani da (Momo) ya ke gabatarwa a gidan Talabijin na Arewa 24. Momo wanda ya shahara wajen iya barkwanci a fina-finan Hausa, ya kunyata ‘yar fim ta hanyar yi mata tambayoyin da a wajen wasu Musulmi za su iya kallonsa babban abin kunya. Ya tambaye ta Wacece ta shayar da Manzon Allah Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam? ‘Ya Za Kai Min Haka? Cikin dariya ta fada ta kuma kasa ba shi amsa. Sannan ya tambaye ta izunta nawa a Alkur’ani mai tsarki? ‘Mu Ba Izu Ake Koya Mana Ba Mu Isalamiyar Mu Kawai Alkur’ani Ake Karanta Mana’. Wajen Hadda Fa? ‘Kawai Mu Karanta Mana Ake Yi’. Mutane da dama sun soki Momo a matsayin yi mata tambayoyin da ba su da alaka da wannan shiri. Sannan wasu na ganin ‘Yar Fim ta yi abin kunya na rashin amsa wannan tambayoyi musamman a matsayinta na mai ikirarin wa’azi.
Download Here

Leave A Reply

Your email address will not be published.