Turmi da tabarya: An kama wani malamin addini yana kokarin ketawa matar aure haddi

3,327

Wani malamin addinin kirista daga cikin daliban babban malamin addinin na kirista Emmanuel Badu Kobi dake shugabantar rukunin majami’un Glorious Wave Chapel International watau Fasto Osofo an kama shi turmi da tabarya da wata matar aure.
A wani faifan bidiyon da yayi ta yawo a kafafen sadarwar zamani da yanar gizo, an ga Faston karara yana fasikanci da matar auren wanda hakan ya haifar da zazzafar muhawara da cece-kuce a tsakanin mabiyan addinin na kirista.

Majiyarmu Hausa wadda wakilinta ya ga bidiyon ta samu cewa Faston yana sanye ne da farar karamar riga da kuma gajeren wando inda kuma jama’ar gari suna ta tozarta shi sakamakon ta’asar da suka tafka. Tun farko dai kamar yadda muka samu, Fasto din yayi kokarin danne matar auren ne yayi lalata da ita da karfi inda ita kuma tayi ihu har jama’a suka zo ceton ta.

Leave A Reply

Your email address will not be published.