Tashar Baro: Buhari zai kaddamar da fara aikin tashar jirgin ruwa na farko a Arewacin Najeriya

513


Duk da yakin neman zaben da ake yi, hakan bai hana gwamnati cigaba da aiki ba, anan ma shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da fara aikin tashar ruwa dake garin Baro a jahar Neja, a ranar Asabar 19 ga watan Janairu.
Majiyar mu ta ruwaito kaakakin hukumar kula da hanyoyin ruwa na cikin gida, NIWA, Tayo Fadile ne ya bayyana haka a ranar Alhamis 17 ga watan Janairu yayin da yake zantawa da manema labaru a garin Lokoja na jahar Kogi.

A jawabinsa, Mista Fadile yace gwamnatin tarayya ta karkare ginin wannan tashar ruwa mai matukar muhimmanci ga al’ummar yankin Arewacin Najeriya da ma Najeriya gaba daya ne akan kudi naira biliyan shida (N6,000,000,000). Ya kara da cewa kamfanin kasar China, CGCC Global Project Nigeria Ltd. ce ta gudanar da aikin ginin tashar ruwan, wanda yace sun sanya na’urar janwe na daukan kaya na zama irin na tafi da gidanka.
Baya ga na’urar daukan kaya, haka zalika an samar da rumfar hutawan jirgin ruwa kafin ya yi gaba, ofisoshin ma’aikata, sansanin tsaftace ruwa, na’urar bada wutar lantarki, da dai sauran gine ginen da ake bukata ta yadda tashar zata yi aiki yadda ya kamata. “Tashar ruwa ta Baron a daga cikin tashoshin ruwan da gwamnatin tarayya ke ginawa a fadin kasar nan don ganin aikin yashe kogin Neja bai tafi a banza ba, ana sa ran zai samar da ayyuka na kai tsaye guda dubu biyu. “Tashar za ta rage adadin manyan motoci masu dakon kaya da mai dake bin manyan hanyoyinmu, wanda hakan zai rage yawan lalacewar hanyoyin.” Inji Tayo Fadile.

Rahotanni sun tabbatar da a yanzu haka an fara aikin inganta hanyar data hada tashar da babbar hanyar garin Agaie ta jahar Neja, garin da Baro ke ciki, don saukaka ma manyan motoci masu daukan kaya.

1 Comment
  1. Abdullahi i.nuhu says

    Allah ya tabbatar da alkhairi

Leave A Reply

Your email address will not be published.