Ko Me Shugaba Buhari Zai Fadawa Zamfarawa Idan Ya Zo Yakin Neman Zabe Na 2019?

149

Ko Me Shugaba Buhari Zai Fadawa Zamfarawa Idan Ya Zo Yakin Neman Zabe Na 2019?

Daga Ibrahim Maazu Mada Bakenawa
Me shugaba Buhari zai fadawa Zamfarawa idan ya zo kamfen na 2019?
Tabbas, jihar Zamfara dai na daya daga cikin jihohin da shugaba Buhari ke da dimbin masoya nusamman a zaben shekara ta 2015 inda ya lashe kusan kuri’un da aka jefa a jihar. Inda Zamfarawa ke cike da fatan idan ya kai ga nasara za su dara ta hanyar kawo masu karshen fashi da makami, satar shanu da dai makamantan wadannan matsaloli.
Domin a lokacin baya babu wanda ya isa ya fadi laifin shugaba Buhari a cikin jihar Zamfara ko mai matsayin sa a gwamnati.
Sai dai tun bayan samun nasarar shugaba Buhari ya yi jifa da Zamfarawa da kuma matsalar da ta sa su gaba. Wanda kawo yanzu matsalar sai rikida kawai take daga mara kyau zuwa mafi muni. Wanda hakan yanzu ya saka shakku ga mafi yawan zukatan Zamfarawa akan gwamnatin shugaba Buhari.
Duk da masifu kala kala da suka addabi jiharmu ta Zamfara amma abun mamaki da ban haushi gwamnatin shugaba Buhari ba ta taba kawo muna agaji ko dai na abinci, sutura, kudi ko kuma ta aiko mana da sakon jaje idan zuwa ya gagara kamar yadda muka ga ana aikawa wadanda ake so a wata jihar.
Tabbas, yanzu mun tabbatar shugaba Buhari Zamfarawa ne kawai ke ta kumfar baki a kansa amma shi ko a baki ba mu kai masa ba balantana mu shiga zuciyarsa .
Abun da dai muka zura ido mu gani shi ne idan ya zo jihar mu ko me zai fada mana dan kara samun goyon bayan mu?
Hatta ‘yan tawayen da aka sace har tsawon sati uku a hannun ‘yan bindiga bai dauki hankalin shugaba Buhari ba duk da ‘yan bindigar sun yi ta barazanar kashe daya daga cikin su muddin aka kasa kai masu kudin fansa.
Allah sarki duniya ashe Zamfarawa ke son shugaba Buhari amma shi ko ajikinsa .
Ya Allah muna tawassali da kyawawan sunayenka masu tsarki ka kawo muna zaman lafiya a jihar mu ta Zamfara. Amin.
Na ku Masoyin Zamfara
07084400431

Leave A Reply

Your email address will not be published.