Fittacen jarumin Bollywood Kader Khan ya rasu

231


Fittacen jarumin Bollywood Kader Khan ya rasu yana da shekaru 81 a duniya bayan fama da rashin lafiya a wani asibiti da ke kasar Canada inji iyalansa. Za ayi jana’izar Khan ne a kasar Canada inda iyalansa suke kamar yadda dansa Sarfaraz ya shaidawa kafafen watsa labarai a Indiya. Khan ya rasu ya bar ‘ya’ya biyu da mata guda daya.
Wadanda suka bayyana alhinin rashin Kader Khan sun hada da Firaministan Indiya, Narendra Modi ta manyan jaruman Bollywood da suka hada da Amitabg Bachchan, Akshay Kumar da Shatrughan Sinha.
Kader Khan ya dade yana rubuta labarin fina-finai kafin ya fara fitowa a fim. Ya rubuta labarin fina-finai da dama da suka yi fice, kamar ‘Coolie’ da ‘Naseeb’ da ‘Aankhen.’ An haife shi na a garin Kabul da ke Afganistan amma daga bisani iyayensa suka koma Mumbai da ke Indiya. Mahaifinsa dan asalin Afganistan ne yayin da mahaifiyarsa ‘yar kasar India ne. Khan ya fara fitowa a fina-finai ne a shekarar 1973 kuma ya fito a fim sama da 300 baya ga rubuta fina-finai kimanin 250. Jarumin ya yi fice a rawar da ya ke takawa a fina-finai na matsayin bos kuma daga bisani ya koma yana wasan barkwanci.

Leave A Reply

Your email address will not be published.