EFCC za ta gurfanar da Diezani a gaban kotu

156

Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati ta ce za ta gurfanar da tsohuwar ministar man fetur ta kasar, Mrs Diezani Alison-Madueke a gaban kuliya kan zargin cin hanci da rashawa.

A sanarwar da mai magana da yawun hukumar Mr Tony Orilade ya aike wa manema labarai ranar Litinin da yamma, ya ce a watan Fabrairun 2019 ne za a gurfanar da Mrs Alison-Madueke da kuma tsohon shugaban kamfanin tatar mai na Atlantic Energy Drilling Company, Jide Omokore kan zargin aikata laifuka biyar.

A cewar EFCC, ana zargin mutanen biyu da karbar hanci da kyautuka a wurare biyu – dukka a birnin Lagos, lamarin da ya saba wa dokar hana karbar hanci da rashawa.

EFCC ta kara da cewa ta samu izinin gurfanar da mutanen biyu a gaban kuliya daga mai sharia Valentine Ashi ta babbar kotun birnin Abuja ranar uku ga watan Disamba.

Hukumar ta nemi izini daga kotun domin ta samu damar taso keyar Mrs Madueke daga Burtaiya inda take zaune tun shekarar 2015.

EFCC ta shaida wa kotun cewa ta dade da aike wa tsohuwar ministar takardar gayyata zuwa Najeriya domin ta kare kanta daga zarge-zargen cin hancin da ake yi mata amma ta ki amsa gayyatar.

Da ma dai hukumar ta dade tana so a ba ta umarnin gurfanar da tsohuwar ministar man a kotun da ke Najeriya.

Tsohuwar ministar na cikin manyan jami’an tsohuwar gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan da ake zargi da cin hanci, ko da yake ta sha musanta zargin.

Ta fice daga Najeriya zuwa Burtaniya jim kadan bayan Muhammadu Buhari ya kayar da Mr Jonathan a zaben 2015.

A watan Aprilun 2016, EFCC ta kwace gwala-gwalan da darajarsu ta kai N593m daga hannun tsohuwar ministar.

Kazalika, a watan Agustan 2017, wata babbar kotun da ke Lagos ta mallaka wa gwamnatin Najeriya kaddarorin Mrs Diezani Alison-Madueke, da suka kai $40, wato kimanin naira biliyan 14.

Leave A Reply

Your email address will not be published.