Dandalin Kannywood: Gaskiya ta bayyana game da soyyar Jamila Nagudu da Mai Mala Buni

1,398


Dan takarar gwamnan jihar Yobe kuma sakataren jam’iyyar APC na kasa, Alhaji Mai Mala Buni ya karyata jita-jitar da ake ta yadawa a wasu kakafun sadarwa na bogi cewa zai auri fitacciyar jarumar finafinan Hausa, wato Jamila Nagudu.
Mai Mala Buni ya ce labarin ba shi da madogara bare tushe, kawai yarfe ne irin na masu adawar siyasa.
A yayin tattaunawarsa da majiyar mu ta jaridar RARIYA, sakataren na APC ya bayyana cewa hoton sa da aka dinga yadawa da jaruma Jamila Nagudu ba wai shi da ita kadai bane suka dauka, sun dauka ne da sauran abokan sana’arta a yayin ziyarar da suka kawo masa a matsayin sa na jigo a jam’iyyar APC. Amma sai aka yanke aka bar iya shi da ita don kawai biyan bukatar masu adawa.

Mala Buni ya kara da cewa yana daga cikin irin gudummawar da mawaka da ‘yan fim suka bayar a wannan gwamnati, irin wakoki da finafinan da suka yi a kan gwamnatin Buhari.

Don haka akwai kyakkyawar alaka taakanin su da ‘yan fim a siyasance.
Sannan kuma irin ziyarar da ‘yan fim din suka kai masa sun kai shugaba Buhari irin ta a Villa ba sau daya ba sau biyu ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.