Dalilina Na Shiga Harkar Fina Finai – Garzali Miko

188


Fitaccen jarumin kuma dan rawa ya bayyana cewa ya fara harkar fina-finan Hausa ne kimanin shekaru sama da goma da suka shude inda a da yake aikin bayar da haske kafin daga bisani ya kara samun matsayi a harkar.
Haka zalika jarumin ya bayyana cewa tsabar sha’awa ce kawai ta jefa shi cikin harkar shi yasa ma ya faro ta tun daga tushe watau a matsayin karami a harkar ya ya zuwa yanzu da ya soma zama fitacce kuma jarumi.
Garzali ya kuma kara da cewa akwai kalubale a harkar ta fim kamar dai sauran fannonin rayuwa da ma duk abinda dan Adam keyi wani lokaci a samu farin ciki wani lokaci kuwa a sami akasin haka.

Leave A Reply

Your email address will not be published.