“Buri na in zama director kafun nayi aure” Jamila Nagudu

182


Babban jarumar Kannywood Jamila Umar Nagudu ta bayyana cewa babban burin ta shine ta zama mai bada umurni a film (director) kafun ta yi aure. Jarumar wadda ta share kimanin shekaru goma a harkan fim ta ce ta samu nasarori a wannan sana’ar da ita kanta ba zata irga ba kuma ba tada wani shiri na gaggawa na barin harkan domin a ganin ta har yanzu tana da sauran rawar da zata taka. Jarumar yar asalin garin Bauchi ta mika sakon godiya ga dukkan masoyan ta kuma ta bayyana cewa har yanzu ba su gama ganin rawar ta ba. Ku kasance da hausaloaded.com zamu kawo muku cikakkiyar hirae da ankayi da ita

Leave A Reply

Your email address will not be published.