Za a maka ‘Dan tsohon Shugaban wata kasa a gidan Yari

99

Za a maka yaron tsohon Shugaban wata kasa a cikin gidan yari – ‘Dan tsohon Shugaban kasar Honduras zai yi shekaru 24 a tsare – An same shi da laifin safarar miyagun kwayoyi na hodar iblis Mun samu labari cewa yaron wani tsohon Shugaban kasar Honduras zai shafe shekara da shekaru a gidan maza.

An samu Fabio Lobo dan gidan tsohon shugaban kasar Honduras Porfirio Lobo da laifin safarar miyagun kwayoyi inda yake kokarin saidawa a kasar Amurka. An yi caraf da shi yanzu haka kuma an yanke masa daurin shekaru 24 a kurkuku.

Alkalin ya yanke masa hukunci mai tsauri inda yace Lobo yayi kokarin amfani da damar sa ta Dan tsohon shugaban kasa wajen shigo da kwayoyin hodar iblis. Shi dai tsohon Shugaba Lobo bai tsaya kokarin kare ‘Dan na sa ba yace ta shi ga fice sa. Kwanakin baya mu ka ji tsohuwar Ministan Najeriya Diezani Madukwe ta koma gidan haya a Birnin Landan. Hakan ya faru ne bayan Gwamnati na ta karbe gidajen ta.

Naijhausa

Leave A Reply

Your email address will not be published.