Za a caji Ramos Euro biliyan 1, saboda dukan Mohammed Salah da yayi

150Wani Lauya dan asalin kasar Misra ya kai karar Sergio Ramos da bukatar ya biya pam biliyan 1 sakamakon raunin da yaji wa shahararren dan wasan kwallon kafar nan wanda tauraruwar shi take haskawa a yanzu, Mohammed Salah, wanda yaji masa ciwo a wasan su na karshe na cin kofin zakarun turai wato Champion's League a turance

Wani Lauya dan asalin kasar Misra ya kai karar Sergio Ramos da bukatar ya biya pam biliyan 1 sakamakon raunin da yaji wa shahararren dan wasan kwallon kafar nan wanda tauraruwar shi take haskawa a yanzu, Mohammed Salah, wanda yaji masa ciwo a wasan su na karshe na cin kofin zakarun turai wato Champion's League a turance.An fitar da Salah yana hawaye sakamakon raunin da ake tsammanin yaji a kafada wanda hakan ya jawo aka danne Liverpool da wuri, inda Real Madrid ta tafi gida da nasarar ci 3-1.

Abinda aka fi tsoro shine Salah ba zai iya buga kwallon kofin duniya ba- Jurgen Klopp yace akwai yuwuwar dan kwallon ba zai iya shiga gasar ba amma dan kwallon yace zai iya.

Lauya Bassem Wahba yace zai cigaba da shigar da karar da yayi niyya kamar yanda ya fada a gidan wani talabijin na kasar Misra.

"Da gangan Ramos yayi wa Mo Salah rauni kuma dole ne ya fuskanci hukunci."

"Na shigar da kara kuma na kai korafi ga hukumar FIFA. Zamu bukaci pam biliyan 1 na raunukan ciki da waje da Ramos ya yiwa Salah da kuma mutanen kasar Misra.

Leave A Reply

Your email address will not be published.