Yarinyar da aka yi ma fyade sau 43,000 (Hotuna)

529

Tashin hankali ba zai misaltu ba musamman ga wannan budurwar da aka yi ma fyade sau dai-dai har sau dubu arba’in da uku (43,000) kuma ake tilasta mata kwanciya da maza 30 a kowane rana.

Karl Jacinto

Ita dai wannan yarinya mai suna Karla Jacinto yar kasar Mexico ce, kuma an sace tane tun tana da shekaru 12 inda ake tirsasa mata shiga harkar karuwanci, dalilin haka yasa take kwanciya da maza 30 kowane rana tun tana yar shekara 16. Karla tace tana da shekaru 12 wani mutum mai safarar mata ya siye ta a hannun danginta bayan ya basu kyaututtuka da kudi, daga nan sai ya kai ta garin Guadalajara, inda a nan ne ta fara karuwanci, sai dai shekarar 2008 jami’an tsaro masu yaki da safarar yan mata suka ceto ta.

A yanzu Karla Jacinto ta kai shekaru 24, kuma ta zama yar karajin kare hakkin mata, inda take ziyartan kasashen don wayar ma yan mata kai dangane da matsalar karuwanci da karfafa ma wadanda aka yi ma fyade gwiwa.
Yayin da take yi ma CNN jawabi, Karla Jacinto tace “sun duka na da ice, suna dukana da wayar wuta, kuma suna dukana da kacan karfe. Tun ina shekara 12 suka tursasa min karuwanci. Sunci mutuncina sosai ba kadan ba” Jaridar Mirror UK ta ruwaito Karla Jacinto tana fadin cewa wasu daga cikin masu zuwa kwanciya da ita yansanda ne, wasu kuma malaman addinai ne, da alkalai.

Comments are closed.