‘Yar Aiki Ta Fasa Kan Maigidanta Yayin Da Ya Yi Yunkurin Yi Mata Fyade

273‘Yan sanda sun damke wata ‘yar aiki bayan da ta ji wa maigidanta mummunan rauni a yayin da ya ke yunkurin yi mata fyade.
Wannan lamari ya faru ne a kasar Uganda.
‘Yar aikin mai suna Nakayanga Rashida ta kwada wa maigidan na ta dutse ne a kai, lamarin da ya sanya shi ya yi ta zubda jini.

Yayin da yan sanda suka sanya mata ankwa, Rashida ta yi ta zubar da hawaye ta na rokon a yafe mata, kamar yadda rahotan ya bayyana.
Toh sai dai babu batun ko ‘yan sandan sun kama maigidan da yunkurin fyade ko kuwa kyale shi suka yi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.