Yansanda sun gayyaci mawakiya sakamakon wallafa hoton tsiraici, karanta abin da ya faru

217

Yansanda a birnin Lusaka na kasar Zambia, sun gayyaci fitacciyar mawakiyar nan Cynthia Kayula Bwala wacce aka fi sani da suna Kay Figo bayan ta wallafa wani hoto da ke nuna rabin tsiraicin jikinta a yanar gizo.
A cikin wannan hoton dai an ga Kay Figo zaune a kan kujera yayin da ta bude kafafunta kuma ta yi amfani da hannunta daya ta rufe al’aurarta domin iya bakin cibiyarta zuwa kasa tsirara ne babu tufa a jikinta.
Mujallar isyaku.com ya gano cewa Kay Figo ta wallafa hoton ne gabanin kaddamar da wani faifen waka da aka yi ma lakabin “Taken” wanda aka saki a kasuwa a ranar da ta dauki wannan hoto, wanda shi ne za a yi amfani da shi a matsayin bangon hoton wannan waka.

Amma kakakin yansanda Esther Katongo, ta ce yansanda sun gayyaci mawakiyar ne domin su ji ta bakinta dangane da wannan hoto, bayan sun yi la’akari da yadda aka baiyyana tsiraicin mawakiyar. Esther ta ce yansanda suna son su fayyace ko mawakiyar ce ta dau wannan hoto a haka ko kuma wasu ne suka yi amfani da kimiyyar hada hotuna suka yi mata wannan aiki.

Comments are closed.