Yan sanda Sun Kama masu safarar Mutane a jihar Osun

104

Wani mai safarar kwarangwal din kawunan jama’a ya shiga hannu – Yansanda sun samu nasarar kama mutumin ne a jihar Osun Rundunar Yansandan jihar Osun ta kama wani mutumi mai suna Adeniyi Adeyeye dauke da kwarangwanl din kawunan mutane a garin Ife, na karamar hukumar Ife. Kwamishinan Yansandan jihar, Fimihan Adeoye yace an kama mutumin ne sakamakon samun bayanan sirri da aka yi ne daga wasu jama’a,kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito shi. Kwamishinan Yansandan yace rundunar na cigaba da gudanar da bincike akan mutumin, sa’annan zasu gurfanar dashi gaban kotun da zarar an kammala bincike.

Da ake tambayar mutumin, yace wani abokin sa Akin ne ya kawo masa kan, inda ya aike shi dashi, sai dai da yaji matsi, sai yace ai aikin tsafin kudi zai yi da kan.

Leave A Reply

Your email address will not be published.