Yan Kannywood sun yi jimamin shekara 12 da mutuwar Ahmad S Nuhu

501

Ana ci gaba da tunawa da shahararren jarumin fina-finan Hausa marigayi Ahmad S Nuhu bayan da ya cika shekara 12 da rasuwa a ranar Talata.

Jarumin ya rasu ne ranar 1 watan Janairun shekarar 2007 sandiyyar hadarin mota a Najeriya.

Hakazalika, a ranar an rika tunawa da jarumar fina-finan Hausa Hauwa Ali Dodo wadda ta rasu a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2010.

Wasu daga cikin masu harkokin fim sun bayyana irin kusancin da ke tsakaninsu da kuma kyawawan halayyarsu.
Ali Nuhu wanda na kusa ne da jarumin ya yi addu’ar Allah ya jikansa da rahma a wani sakon cika shekara 12 da rasuwar Ahmad S Nuhu, wanda ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Talata..
Hakazalika ya yi fatan Ubangiji ya yafe wa Hauwa Ali Dodo dukkan kura-kuranta ita ma a wani sako da ya wallafa na cikarsa shekara tara da rasuwa.
Darakta kuma jarumin fina-finai Falalu Dorayi ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa: “Shekaru 12 kenan da rashinka. Allah yai maka Rahma AHMAD S. NUHU (amadu) Allah ya sanya haske da ni’ima a kabarin ka.”

Shi ma Baballe Hayatu ya yi addu’ar Allah ya jikan Hauwa Ali Dodo.

Haka dai jama’a da sauran masu ruwa da tsaki a Kannywood suka rika aike wa da sakon tunawa da jaruman biyu.

Comments are closed.