Yakamata Kannywood Su dinga koyi da Bollywood

223

BOLLYWOOD VS KANNYWOO

Mundade muna kira ga abokanmu na masanaantar KANNYWOOD da suyi amfani da irin salon yadda BOLLYWOOD take tafikar da finafinan ta tunda muma yanzu muna da kayan aiki na zamani da kuma kwararrun jarumai.

To akaro na farko da daya daga cikin Iyayen wannan kungiya tamu ta Bollywood fans mai albarka wato Director Hafizu Bello ya bujiro da irin wannan aiki Mai nagarta acikin Film din daya bada Umarni mai taken HAKKI wanda kamfanin Hamisu Lamido Iyantama ya dau nauyi, kuma kwararran jarumi mai tashe Abdul M. Shareef ya baje iyawarsa aciki.

Film ne dayazo da labari akan rikicin Masu Kamfani da kuma Yan kwadago… Wannan Film yazo da darasi na irin kacaniyar da matsaloli da Yan kwadago suke fama da ita… Idan da wanda yake aiki a kamfanonin fata na Sharadha ko Chalawa to tabbas yasan akwai labarin daya cancanci duniya tasani akai.

Muna kishin masanaantar kasar mu yankin mu suma su kasance cikin jerin zakarun gwajin dafi.

Daga:Usman Solo

Comments are closed.