Yajin aiki: Kungiyar ASUP ta bi sahun ASUU

208

A yayin da har yanzu ake kan teburin sulhu tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) a kan yajin aikin sai baba-ta-gani da kungiyar ta shiga tun watan Nuwamba, sai gashi kungiyar malaman makarantun kimiyya na kasa (ASUP) ta bi sahun ASUU.
Kungiyar malaman makarantun kimiyya na kasa (ASUP) ta bayyana cewar ta yanke shawarar tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar Laraba, 12 ga watan Disamba. Ma’ajin kungiyar, Suleiman Usman, ya sanar da hakan yayin ganawa da manema labarai bayan kammala wani taron shugabannin kungiyar a jiya, Juma’a. Ya bayyana kungiyar dauki wannan mataki ne bayan tattaunawa ta tsawon lokaci a Kaduna Polytechnic.
Shugabannin kungiyar ASUU Usman ya kara da cewar zasu shiga yajin aikin ne saboda gazawar gwamnatin tarayya na cika alkawuran da ta dauka a cikin yarjejeniyar da suka cimma tun shekarar 2016. Ya zargi gwamnatin tarayya da yin kunnen uwar shegu da gargadin kungiyar na shiga yajin aiki cikin kwanaki 21 matukar gwamnatin bata yi wani hobbasa wajen kara wa makarantun kudaden gudanarwa ba.
Ma’ajin ya ce kungiyar ASUP ta bawa gwamnatin tarayya isashshen lokaci domin cika alkawuran da ta dauka, yana mai bayyana cewar kungiyar bata da wani zabi da ya wuce ta shiga yajin aikin sai baba-ta-gani. Kazalika ya ce shiga yajin aikin ranar Laraba ya yi daidai da karewar wa’adin da suka diba na kwanaki 21. Kungiyar ta umarci dukkan mambobinta dake fadin kasar nan da su shiga yajin aiki daga karfe 12:00 na daren ranar Laraba ta sati mai zuwa.

@NaijHausa

Comments are closed.