Yadda mukeyi da kudinda muka karbo daga Barayin gwamnati-Gwamnatin nigeria

104


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da sanarwar cewa, gwamnatinsa ta na amfani da wani kaso na kudaden da aka karbo daga hannun masu satar dukiyar gwamnati wajen marawa kasafin kudi na 2017. A ranar Talata 10 ga watan Oktoba, Shugaban lissafin kudi na kasa baki daya Alhaji Idris Ahmed, wanda ya wakilci shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wurin wani taron masana lissafin kudi da aka gudanar a birnin Tarayya. Shugaban ya bayyana cewa, gwamnati ta na amfani da wani kaso na kudin da ta karbo daga hannun wadanda suka sace dukiyar gwamnati domin marawa kasafin kudi na 2017.
A kalaman shugaban kasar, “gwamnatinsa ta yi hobbasa kwarai da aniyya wajen habaka tattalin arzikin kasa”.

KARANTA:- Budaddiyar Wasika zuwa ga Abubakar Shekau, daga Mubarak Bala

“Idan aka duba karfin samar da wutar lantarki ya karuwar da bai taba yi ba a tarihi zuwa ma’aunin wutar lantarki 7001 na megawatts, wanda muke sa ran ya zai karu zuwa ma’auni 10, 000 na megawatts a shekarar 2020”. Idris ya kara da cewa, samar da asusun gwamnati guda a watan Satumba na shekarar 2015 domin ajiyar dukiyar gwamnati ya taimaka kwarai wajen fayyace komai a fili musamman yadda gwamnatin take gudanar da al’amurran dukiyar al’umma.
Naijhausa

Leave A Reply

Your email address will not be published.