Ya kamata a kyale ni haka – Benzema

178

Dan wasan gaba na Real Madrid Karim Benzema ya musanta rahotannin da ke cewa yana da hannu a wani yunkuri na sace wani mutum a Paris, yana mai cewa ”ya kamata a bar ni na huta haka”.

Wata jaridar Faransa, mai suna Mediapart ta bayyana cewa Benzema mai shekara 30 yana daga cikin mutanen da suka yi yunkurin sace mutumin wanda tsohon eja ko wakilinsa ne mai suna Leo D’Souza, wanda aka ce Benzeman na binshi euro dubu 50.

Mutumin ya yi zargin cewa Benzema da wasu mutane sun yi kokarin sa shi a sundukin wata bakar mota a ranar 7 ga watan Oktoba.

A wani rubutu da ya yi a Twitter Benzema ya ce: ”Anya da gaske ake a wannan duniyar kuwa?”
Ya kara da cewa: ”Dole ne a daina da wannan.”

Kamar yadda rahoton ya nuna, mutumin da ya yi zargin ya sheda wa ‘yan sanda cewa ya ga Benzema a bayan motar.

Amma kuma rahoton ‘yan sanda na baya bayannan ya ce ana ganin dan wasan ba ya wurin a lokacin, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayyana.
Wasu kafofi sun bayyana wa kamfanin dillancin labaran cewa masu gabatar da kara a Paris sun fara gudanar da bincike a kan matukin motar a kan zargin yunkurin satar mutumin.

Rabon da Benzema ya yi wa Faransa wasa tun bayan da aka ki sanya shi a tawagar kasar ta gasar cin kofin kasashen Turai ta Euro 2016.
BBC ta tuntubi kungiyar dan wasan Real Madrid a kan wannan zargi da aka yi masa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.