WURAREN DA YA HALATTA A SAKI MACE MAI HAILA

213

*_WURAREN DA YA HALATTA A SAKI MACE MAI HAILA_*

*Tambaya*
Akaramakallah na ji an ce haramun ne a saki mace mai haila, to amma wani lokacin za ka ga kun samu rashin jituwa da matarka ta yadda baza ka iya jiran lokacin tsarkinta ba, to malam akwai wasu lokuta ne da aka halattawa mutum ya saki matarsa ko da tana haila?

*Amsa*
To dan’uwa tabbas Allah ya yi umarni da kar asaki mace sai tana da tsarki kamar yadda yake cewa “Idan za ku saki mata to Ku sake su afarkon iddarsu) ma’ana a tsarkin da baku take su ba, Addalak aya ta: (1) saidai akwai wurare guda uku da ya halattta a saki mace mai haila:

*1*. Idan sakin ya kasance kafin ya kadaita da ita ko kafin ya sadu da ita, to anan ya halatta ya sake ta tana haila.

*2*. Idan ta yi hailar ne tana da ciki.

*3*. Idan ya sake ta ne bayan ta fanshi kanta, to anan ya halatta ko da tana haila, saboda Annabi (S.A.W) bai tambayi matar Thabit ba shin tana haila ne ko tana da tsarki, lokacin da zata yiwa mijinta kul’i, kamar yadda Bhukari ya rawaito ahadisi mai lamba ta: 5273.

Duba: Dima’uddaabi’iyya shafi na: 33.

In ban da wadannan wurare, to bai halatta a saki mai haila ba, kuma in har an sake ta, to sakin bai auku ba a wajen wasu malaman.

Allah shine mafi sani.

21/04/2017

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Comments are closed.