Wasu Abubuwa 10 Dake Sa Maza Gudun Mata Bayan Sunyi Jima’i da Su.

24,731

Tunda dai yanzu kin fahimci cewa duk irin jima’i da kika yi da namiji bai gama dake ba kamar yadda bincike ya tabbatar. Kuma binciken ya kara tabbbatar da cewa ba wai saboda saninki da yayi bane yasa ya daina kulaki ko ya daina zuwa koma ya fasa aurenki da yayi alkawari. Duk da haka da akwai wasu dabi’u da halayen da mace zata yi namiji ya gujeta bayan yayi jima’i da ita.

Wannan matsalar na gudun mata bayan yin jima’i dasu bawai ya tsaya bane kadai tsakanin masoya mazinata kadai ba, hatta matan aure suna kokawa da yadda mazajensu suke gudunsu bayan yin jima’i dasu. Wasu matan sun tabbatar da cewa mazajensu na daukan lokuta mai tsawo kamin suyi jima’i dasu, wasu ma idan sunzo yi babu wani armashi haka nan zasu yi su tashi. Matan aure kenan da ya zamewa mazajensu dole su biya musu bukata irin na jima’i.

Su kuwa masoya ‘yan cuwa-cuwa kina bashi sau daya baki sake ganinsa duk lokacinda kika kira wayarsa sai dai ya fada missed calls. To ga wasu dalilai nan da suke jawowa ki duba watakila kinada matsala a guda daga cikinsu. Domin ko wanne cikinsu zai iya jawowa namiji ya gujeki.

1: Dabi’a: Da akawai wasu mazan, duk irin son da suke miki, duk hidimar da zasu miki, suna kwanciya dake sau daya kin fita musu a rai. Bazaki sake ganinsu ba ko sake samun wata damar yin jima’i dasu.

Ba a harkar zina ba kadai, da akwai irin wadannnan maza a cikin mazan aure, wanda da zaran sun auri mace suna kwanciya da ita daga nan ko dai saki ya biyo baya bayan wasu lokatai ko kuma tayi ta zama a haka babu jima’i. Irin wadannan mazan suke ake yawan ganinsu suna aure su saka wanda masu iya magana ke kiransu da suna ‘auri saki’ ko masu auren dandano.

Maza masu irin wannan dabi’ar babu yadda kika iya dasu illa idan kinyi kuskuren fadawa tarkonsu sai ki dauki darasin kare kanki nan gaba.

2: Sana’a Ko Aiki: Akwai wasu mazan da yanayin aikinsu ko sana’arsu na kyamar barin wani ya kusancesu domin gudun kada ya san halin da suke ciki, irin wadannan mazan basu cika son yi soyayya ba, idan suka yi sha’awar mace kuma suka sameta yanada matukar wahala su sake kulata saboda gudun janta a jikin harma tasan halin da yake ciki. Masu wannan dabi’an sunfi yiwa mata na waje musamman matan bariki. Don haka ba abun mamaki bane daga yi sau daya bazaki sake ganinsa ba.

3: Sirri: Mazan dake neman mata a waje suna bukatan sirri, ko dai domin matsayinsu cikin al’uma ko kuma domin boye abunda yake yi wanda yasan ba mai kyau bane.

Irin wadannan mazan idan suka fahimci macen da suka dauko mai surutu ce, wacce zata iya zuwa ta fadawa duniya tsakaninsu to suna afka mata na wannan lokacin bazata sake ganinsa ba barema ta sake samun damar yin wani mu’amala dashi.

4: Tsafta: Maza dayawa ma’aurata, ‘yan bariki da masoya suna gujewa matansu bayan sun sadu dasu sau daya. Matan aure kazamai dai duk da wani lokacin mazan na rude idanuwa suci kar su mutu, basa samun gamsuwa irin na jima’i da ya kamata su samu daga wajen mazajensu. Su kuwa wadanda babu lalle babu dole ana samunsu da kazanta shi kenan baki sake ganinsa.

5: Bukatu: Wasu mazan na bariki dana soyayya suna gudun macen da take yawan bijiro da bukatun da suke da yawa ko kuma suka fi karfinsu, don haka zai yi likimo yana lallabaki duk randa ya samu ya afkamiki sai dai ya barki da missed calls. Kiyi ta mamaki irin yadda yake miki hidima a baya amma gashi daga bashi ya daina kulaki. Fahimta yayi bakida wadatar zuci idan ya ci gaba da hulda dake zai galabaita.

6: Matsayinku A Jima’ince: Wannan matsalar yana faruwa ga matan aure dana waje. Idan namiji ya fahimci a farkon yin jima’i kinfi karfinsa ko yafi karfinki da wuya ki sake ganinsa. Idan mai son yin jima’i ne sosai ke kuma bakiso ko kina son shi kuma bayaso to zai iya guduwa ko da kuwa aurenki yake yi.

7: Garkuwa; Wasu matan burinsu su yi jima’i dana mijine domin samun wani garkuwa daga gareshi. Idan matan aurece burinta tayi ciki ta haifi namiji shi mijin ya mutu ta ci gado. Da zaran namiji ya fahimci manufarta kenan yana iya kauracemata wanda hakan idan ba ayi dace ba aure ya mutu.
Wasu matan kuwa so suke suyi jima’i da namiji su ce masa ya musu ciki domin su tozartashi ko kuma burinsu suyi bidyo ko hoton tsiracinsu domin neman wani biyan bukata. Da zaran namiji ya fahimci haka bayan jima’i Ku na fako guduwa zai yi.

8: Rashin Ni’ima. Wasu matan bawai ni’imar bace kadai basu dashi, duk lokacin da namiji ya sadu dasu sai ji mass ciwo ko sai ya sha wahala. Maza na samun Kansu a irin wannan matan guduwa suke a haduwar farko.

9: Rashin Iya Jima’i: Kama daga wasanni motsa sha’awar, zuwa yanayin kwanciyar na jima’i. Irinsu kukan kissa, rashin iyasu nasa wasu mazan su guru bayan kwanciyarsu da mace. Idan kuwa matan aurece ba a lokacin da take bukatan jima’i ba zata rika samu.

10: Rashin Kamun Kai: Wasu mazan da zaran sun fahimci basu kadai bane suke zina dake bayan haduwarku na farko to bazaki sake ganinsu ba. Burinsu ya zama su kadai ne suke Jima’i dake.

Sharhi

Yanada kyau ‘yan mata su fahimci cewa a dai-dai lokacinda kuke aikata ba dai dai ba kina iya maids ba dai dai din nan ya zama dai dai. Kada yasa zina kawai kika Santa a gaba da saurayinki babu tunanin yadda zai bijiro da wasu dabi’u da halayen da zai dawo yaji kin fi da cewa da aure bada iskanci ba. Amma idan kika dauka tunda soyayya irin na yasa zina kukeyi don haka duk rashin mutunci da rashin tarbiyan daya kama zaki iya yi ko a ina kuma ko a gaba ways, tofa kina cutan kanki ne. Domin na kusa dake, na kusa dashi sune zasu soma kusheki kinaji kina gani ya barki yake ya auro wata.

Shi dai harkar soyayya mai gaurayi da zina ko nace zinar da kansa abune da har duniya ya tashi baza a daina ba. Yana kuma da kyau cikin yinsa a fahimci haramcinsa da hanyar rabuwa dashi ko kauce masa. Da fatan mata zasu rika natsuwa suna fahimtar abubuwan da suka kamacesu mai makon biyewa son rai.

Comments are closed.