Tarihin Andaluz: Tsohuwar Daular Musulunci Da Ta Wanzu A Spain

200

Yarima Abdurrahman ya kara azama a kokarinsa na shiga yankin Andaluz, duk da dai bai san halin da zai samu kansa ba saboda rikita-rikitar da ake fama da ita a yankin. Sarkin Andaluz dai Yusuf Al-fihiri dan kabilar Berber ne, an ce ya samu sabani da wazirinsa kuma sirikinsa mai suna Al-Sumayl ibn Hatim Al-kilabi wanda ya fito daga wata kabilar Larabawa da ke Sham (Syria) mai suna Shamiyum. Har sun fara yaki a tsakaninsu. A Rundunar waziri Sumayl akwai yawa-yawan mutane masu kyakkawar alaka da Umayyawa, don haka Yarima Abdurrahman yake tsammanin zai samu mafaka a wannan runduna. A kan haka ne Abdurrahman ya dakata a Afirka kusa da garin Sebta, sannan ya tura yaronsa Badar domin ya je ya nemo masa izinin shigowa wannan runduna ta Sumayl da ke Andulus. Badar ya zo Andaluz, ya samu kwamandojin yakin dakarun kabilar Shamiyum guda uku, Ubaidallah Ibn Uthman da Abdullahi ibn Khalid wadanda dukkan su ‘yan asalin garin Damaskus ne kuma ‘yan kabilar kaisu wadanda suke jinsi daya da Umayyawa, sai kuma na ukunsu mai suna Yusuf ibn Bukht wanda ya fito daga garin kinnasrin. Dukkan su sun amince da zuwansa, amma sai suka ce ba su da ikon sahale masa ya zo har sai an jira izini daga babban kwamanda Waziri Sumayl wanda a lokacin yake zaune a Zaragoza. A cikin rashin sa’a, da aka aika wa Sumayl, sai ya ji tsoron idan har Yarima Abdurrahman ya shigo rundunarsa, nan gaba shugabanci zai nema, kuma sai ya danne shi. Don haka sai ya ce sam bai yarda ba. Sai dai kuma da kwamandojin kabilar kaisu suka ji labari, sai suka sanar da Bedar cewa ya sanar wa Abdurrahman cewa su a shirye suke su taimake shi kuma su goya masa ba. Domin a cewarsu, da su rinak yi wa Larabawan Shamiyum biyayya karkashin jagorancin Sumayl, ko su yi wa Laraban Firhiyyun biyayya a karkashin Sarki Yusuf Al-fihri, zai fi kyau su bi dan kabilarsu Abdurrahman, domin farfado da sunan Umayyawa, in ya so komai zai faru ya faru. Da wannan sakon Bedar ya isa ga Yarima Abdurrahman kuma. A kan haka sai Abdurrahman ya shirya bin wasu mutane masu son shiga kasashen Turai don tafiya zuwa Andaluz. An ce daf da tafiyarsa ta cikin jirgin ruwa wasu kauyawa ‘yan kabilar Berber suka tare shi a hanya, sannan suka ce sun kama shi za su yi garkuwa da shi, matsawar yana son fita daga Afirka sai dai ya fanshi kansa. Ala tilas ya fanshi kansa da zinare. Bayan ya dauka ya ba su sannan ya shiga jirgin ruwa don tafiya. Wadancan kauyawa suna tafiya, sai kuma ga wata zugar ta iso, ita ma ta ji labarin Abdurrahman zai bar Afirka zuwa Turai, don haka suka garzayo karbar ganima a wurinsa, amma kuma aka yi rashin sa’a sun zo a makare, tun da har jirgin nasu ya fara tafiya a kan ruwa. Shi ne kuma har wani daga cikin kauyawan ya yi kokarin tsayar da jirgin ta hanyar shiga cikin ruwa da rike igiyar jirgin da hannunsa, yana kokarin tsayar da shi. Amma kafin ya samu nasara, sai aka samu wani daga cikin matukan jirgin ya sare hannun mutumin. Jirgi ya mika da tafiya, suka bar shi nan yana ruri. A karshe dai, Abdurrahman ya samu damar sauka a wani waje da ake kira Almunekar, da ke Gabashin Malaga, cikin yankin na Andalus, a watan Satumba na shekarar 755. Da saukarsa sai kwamandojin nan biyu na kabilar kaisu da ke cikin tawagar Sumayl, wato Abu Uthman da ibn Khalid suka yo hawa tare da mahaya guda dari uku ‘yan kabilar kaisu da wasu na kabilar Shamiyum, suka tarbe shi. Sannan ne aka ce labari ya rinka bazuwa cikin garin Malaga, ana fada wa mutane su fito su tarbi Yarima, wanda ake tsammanin ya rasu, ashe yana raye. Nan da nan kuwa ya zamo mai farin jinin mutane, aka rinka zuwa masa da kyaututtuka, a nan ne ma aka ce wani ya yi masa kyautar wata kyakkyawar baiwa, amma daga baya sai ya maishe ta ga ubangijiyarta. Kuma an ce a iya zamansa a Malaga, sai da ya tara ‘yar karamar runduna ta sadaukai masu jiran umarninsa. Abu kamar wasa, sai ga shi labarin zuwan Yarima Abdurrahman ya bazu cikin Andulus kamar wutar daji. Wannan yasa Sarki yusuf Al-fihiri da waziri Sumayl suka hada kai, domin su ga kurar da za ta kau da su ta taso, sai suka fara shirya shawarar yadda za su yi wa Yarima Abdurrahman gadar zare su dusasar da shi ko su hallaka shi. A karshe suka shawarta cewa su yi masa tayin auraen ‘yar gidan Sarki Yusuf Al-fihiri, idan kuwa ya ki, kawai su kashe shi. Sai dai abin da ba su sani ba shi ne, Yarima Abdurrahman yana da matukar wayau da hangen nesa, don haka duk ya tsammaci muguwar manufa daga gare su. Ana cikin haka, sai fada ya barke a Zaragoza. Wasu ‘yan tawaye masu fafutikar neman mulki suka hada runduna suna yakar dakarun Waziri Sumayl. Wannan yasa Sarki Yusuf din da Waziri Sumayl suka hada karfi domin yakar ‘yan tawayen. Hakan kuma sai ya bai wa Abdurrahman damar kara samun wurin zama da kuma karin dakaru masu yi masa biyayya. shi ne ma aka ce a watan Maris na shekarar 756, Yarima Abdurrahman ya kame garin Sebilla ba tare da wani hargitsi ba. Sarki Yusuf Al-fihiri ya yi niyyar zuwa Sebilla don korar Abdurrahman, amma sai wani fadan na ‘yan tawaye ya kara tasowa a garin Pamplona da ke karkashin masautar Andalus din dai, ga kuma wancan na Zaragoza ba a kammala ba. Sai ya zamana yana cikin tsaka mai wuya. Da fari, ya fara maida karfinsa ne don ganin ya ci nasarar murkushe ‘yan tawaye, amma da abin ya gagara, sai kawai ya yanke shawarar juyowa kan Yarima Abdurrahman da yaki.

Comments are closed.