Ta Yanke Mazakutar Saurayinta Don Ya Sake Bidiyonsu A Yayin Suke Jima’i

401

Ta Yanke Mazakutar Saurayinta Don Ya Sake Bidiyonsu A Yayin Suke Jima’i

Wata mata ta yanke mazakuntar saurayin da almakashin lambu don ya sake bidiyonsu a yayin da suke jima’i.

Wannan abun al’ajabin ya faru ne a kasar Argentina, inda aka gurfanar da wata mata, Brenda Barattin, a kan zargin yankewa saurayinta mazakuntarsa saboda ya nunawa abokansa bidiyonsu da suka dauka a yayin da suke jima’i, inji rahotanni.

Yar shekaru 26 Barattini, ta aikata ne a yankin Nueva Cordoba da ke birnin Argentina a watan Nuwamba na shekarar da ta gabata, wanda hakan ya sa saurayinta dan shekaru 30 ya rasa kashi 90% na mazakuntarsa, sannan ta saka shi cikin wani mummunar hali.

Barattini, wacce ta ke garkame a gidan yari ba tare da beli ba kafin saurarar karan ta a kotu, ta ce sakar bidiyon da saurayinta, Sergio Fernandez, yayi ya jawo ma a raunin tabin hankali.

Na yanke masa mazakunta ne amma ba ga baki daya: Na dan ji masa rauni ne. Ba duka na cire ba: na ji masa rauni ne kawa,” ta ce.

A halin yanzu mutumin na fama da wani hali, inji lauyarsa, a yayin da ya ke jiran likitoci su yi masa aiki.

A cewar kafafen yada labarai na Fox News, ma’aikatan kiwon lafiya sun kasa dinke mazakutar Fernandez da budurwar na sa ta cire.

Abun yayi daidai da karar, Loren Bobbitt, matar da ta yankewa mijinta mazakutarsa a shekar 1993 a yayin da ya ke bacci.

Bobbit ta ce ta yi hakan ne saboda mijinta na ma ta fyade.

Comments are closed.