Ta kasa mijinta a kasuwa zata sayar saboda muzguna mata da yake

722

Wata ‘yar kasar Jamus ta yi gwanjon mijinta a kudi yuro 18 kacal a wani shafin intanet na saye da sayarwa mai suna eBay saboda bakanta ma ta.

Matar wacce mazauniya ce ta birnin Hamburg na kasar Jamus kana mai amfani da sunan sirri “Dorte L” a shafin na eBay ta yi gwanjon mijin da ta aura shekaru bakwai da suka gabata,saboda ta gaji da zama da shi kuma yana bakanta ma ta a kulli yaumin.

A yayin gwanjon matar wacce ba a bayyana ainahin sunanta na gaskiya ba ta gudanar talla kamar haka: “Ga tsohon miji ga duk mai saye.Yanzu kam na gaji da shi.Bai da tsada,kyuata ce ruwan Allah”.

Matar ta bayyana cewa mijinta bai san da cewa ta yi gwanjon sa ba a shafukan intanet duk da cewa labarin ya fito a jaridar Abendatt ta kasar Jamus.Haka zalika ta kara da cewa ta samu mutane da masu dumbin yawa wadanda ke son su saye shi nan take”.

TRThausa.

Comments are closed.