Sunaye: Manyan jaruman Kannywood dake cikin kwamitin kamfen din Aisha

810


A ranar Talata da 1 ga watan Janairun 2019 ne uwargidan shugaban kasar Najeriya, Asiha Buhari ta kafa kungiya da zata taimaka wurin tallata mai gidanta, Shugaban kasa Muhamadu Buhari gabanin babban zaben 2019.
Daily Trust ta ruwaito cewa Aisha Buhari za ta jogaranci kungiyar yakin neman zaben ne tare da uwargidan mataimakin shugaban kasar Najeriya, Dolapo Osinbajo.

Kamar yadda aka saba a kowanne shekara, ‘yan siyasa ne hadin gwiwa da fitattun mutane musamman ‘yan wasan kwaikwayo da ke da al’umma domin taya su yakin neman zabe.
A wannan karon, Aisha Buhari ta zabo wasu fittatun jaruman Kannywood da za su taya ta yakin neman zaben.

Ga sunayensu kamar haka:

1. Ali Nuhu

2. Adam A. Zango

3. Fati Abdullahi Washa

4. Halima Atete

5. Asiya Ahmad

6. Rukayya Dawaiyya

7. Maryam Yahaya

8. Fati S.U.

9. Bilkisu Abdullahi
10. Hannatu Bashir

11. Ali Isa Jita

12. Husainin Danko

13. Baban Chinedu

Comments are closed.