Sojoji sun mamaye kamfanin jaridar Daily Trust gida da waje

253

Sojoji da jami’an tsaro na cikin gida DSS sun mamaye ofisoshin kamfanin jaridar Daily Trust a Abuja da Maiduguri.

A lokacin da wakilin BBC ya isa ofishin a Abuja, ya taras da sojojin da kuma wasu jami’an tsaro sanye da farin kaya sun zagaye ofishin inda suka hana shige da fice.

Mataimakin babban editan jaridar Mahmud Jega ya fada ma BBC cewa sojojin sun isa ofishin da kimanin karfe 4 na yamma, kuma sun kutsa ciki da karfe 5.33.

“Sojoji sun rufe ofishinmu na Maiduguri da safiyar yau, kuma sun tafi da wasu ma’aikatanmu biyu. A halin yanzu suna tsare da su a can”.

Har yanzu babu wani bayani daga jami’an sojoji ko na jami’an DSS game da dalilinsu na kai wannan samamen.

Daga nan sojojin sun bukaci dukkan ma’aikatan su taru a wuri guda kuma sun gudanar da bincike akan ma’aikatan da ke cikin ofis.

Binciken da wakilin BBC ya gabatar ya tabbatar da sojojin sun kai wa jaridar ta Daily Trust wannan samamen ne saboda babban labarin da ta wallafa yau Lahadi a shafinta na farko.

“Sun bukaci dukkan ma’aikatanmu su fice daga harabar ofishin, kuma sun kwace dukkan na’urorin aiki a hannun ma’aiakatan namu”, inji Mahmud Jega.

Har lokacin da ake hada wannan rahoton sojojin na cikin harabar ginin kuma sun kashe wutar ginin baki daya.

Sai dai wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar na cewa, jami’an tsaron sun je ofishin Daily Trust ne don gayyatar wasu ‘yan jaridarta game da wnai labarai da suka wallafa kan wasu shirye-shiryen aikinsu.

@BbcHausa

Comments are closed.