SHIN YA HALLATTA MACE TA YI AIKIN GWAMNATI

191

*SHIN YA HALLATTA MACE TA YI AIKIN GWAMNATI ?*

*Tambaya*

Assalamu alaikum. Malam na ji wasu suna haramta aikin gwamnati ga mata, menene gaskiyar magana akan haka ?

*Amsa*

Wa’alaikumus salam
To ‘yar’uwa Allah Madaukakin sarki a cikin suratul Ahzaab ya umarci mace da ta zauna a gidanta, kar ta dinga yawan fita.

Malamai suna cewa bai halatta mace ta yi aiki a wajan gidanta sai da sharuda guda biyu:

*1.* Aminta daga cakuduwa da maza, kasancewar mace tana da rauni, Kafada-da-kafada da maza yana iya kaita zuwa ga lalacewar tarbiyya.

*2.* Bukata zuwa ga aikin, kamar ya zama ta fito daga dangi matalauta ko kuma mijinta ya mutu tana bukatar abin da za ta tafiyar da bukatun marayunta, ko ya zama aikin likitanci ne a bangaren lalurorin mata.
Kissar Annabi Musa a cikin suratul Kasas lokacin ta ya je Madyana ta yi nuni zuwa ga sharudan da suka gabata.

Idan ya zama dole sai mace musulma ta yi aikin gwamnati ya wajaba ta kula da abubuwa biyu:

*1.* Sanya sutura mai rufe dukkan jiki.

*2.* Takaita magana da maza sai gwargwadon bukata.

Da yawa daga cikin matan da suke aikin gwamnati suna tozarta tarbiyyar yaransu, wasu kuma suna butsarewa mazajansu, saboda idonsu ya bude ta hanyar hira da abokan aiki.

Mutukar miji zai iya daukewa matarsa dukkan bukatunta na dole, to zamanta a gida ta kula da iyalanta da mijinta shi ne daidai, kamar yadda Allah ya umarce ku da hakan a aya ta (33) a suratul Ahzab.
Allah ne mafi sani

*Dr. Jamilu Zarewa*

12/10 /2018

Comments are closed.