Shin Ya Halatta In Auri Matar Da Nayi Zaman Dadiro Da Ita?

430

Assalamu alaikum, Malam ya halarta musulmi ya musuluntar da matar da yayi zaman daduro da ita bayan hakan ya aure ta, limanmin da ya goyi bayan hakan yayi daidai?
” Amsa: Wa’alaikum as salam, ya halatta sabida babu alaka tsakanin dadironsu da auransu bayan ta musulunta Mutukar sun tuba, saboda musulunci yana rusa abin da ya gabace shi na zunubi kamar yadda ya tabbata a hadisin Amru bn Al’ass.
Idan musulmi ya yi zina ya tuba, to Allah yana gafarta dükkan zunuban da suke hakkinsa ne, kamar yadda
[ aya ta:53 a suratu Zumar] ta tabbatar hakan Allah ne mafi Sani.

Comments are closed.