Sarkin Kano Ya Baiwa Nazir Ahmad Sarautar Sarkin Wakarsa

233

Nazir Ahmad wanda ake wa lakani da sarkin waka ya zama sarkin wakar na hakikan domin kuwa Mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya bashi wannan sabuwar sarauta.

Nazir dai dama ya dade ya na rerawa sarkin wakoki masu armashi kuma wadanda suke cike da basira.

Danburan Kano shi ya tabbatar wa mawakin batun bashi sarautar a cikin wata takarda da aka aika masa daga fadar sarki.

Takardar ta bayyana cewa, “Mai martaba ya umurce ni da na yi maka godiya bisa biyayya da soyayya da ka ke masa tun yana Dan Majen Kano har Allah ya sa ya zama Sarkin Kano wannan abin a yaba maka ne.”

Sanarwar ta kara da cewa za a yi nadin sarautar ne a ranar Alhamis 27 ga watan disamba a fadar mai martaba sarkin Kano.

Comments are closed.