Sakon Rabiu Kwankwaso Ga Magoya Bayansa

84

Sakon Rabiu Kwankwaso Ga Magoya Bayansa,
…Kwankwaso Ya Umarci Magoya Bayansa Da Subi Tafiyar Atiku..
Sen Rabiu Kwankwaso, haka Allah ya kaddara saboda haka inakira ga magoya bayana da kukasance masu godewa Allah a duk halin da kuka sinci kanku domin shi lamarin Allah ba’a fushi dashi, duk abunda Allah yayi mana daidai ne, kafin a fara munce Allah ya zaba mana Wanda yafi alheri, yanzu kuma sai muce Allah yasa haka shine mafi alheri.

Ya kuma kara da cewa mu dauki kaddara mu marawa Atiku Abubakar baya tunda shi Allah ya zaba, bawai muyi fushi da zabin Allah ba.
Ya kuma gargadi Magoya bayansa da kada kowa ya biyewa abinda yan adawa zasu fada koyay posting akan rashin nasararsa domin shi da Atiku duk mutum daya ne tunda dukkansu yayan jam’iyar PDP ne
Ya kuma yi fatan Allah ya bawa Atiku Abubakar nasara a zaben General Election dama sauran yan takarkari na jam’iyar PDP baki daya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.