Sakin Bidiyon Ganduje Na Karbar Rashawa Bai Yimun Dadi Ba – Inji Kwankwaso

150


Tsohon gwamnan jihar Kano kuma sanatan Kano ta tsakiya Mai ci a halin yanzu Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana rashin jindadinsa akan bidiyon dake yawo a kafafen sada xumunta na zamani wanda ke nuna gwamnan jihar Kano Ganduje na karbar rashawa.

Ga kadan daga cikin abinda Sanatan ya fada:

“Na samu labarin bidiyon tun kafin su sake shi. Kuma na kira su na ce kar su sake shi. Saboda faifan bidiyon illa ne ga jihar Kano, Hausa Fulani, ‘yan Arewa da ma musilmi baki daya.
Sun saki bidiyon ne a lokacin da muke rigimar fitar da Dan takarar Gwamna.
Nayi yaki da sakin bidiyon ne saboda ina da yakini cewa za mu ci zabe ko babu faifan bidiyon.

Haka kuma, kwankwaso a hirarsa da Dala FM radio Kano ya kara da cewa:
“Bana goyon bayan sakin faifan bidiyon, saboda ba iya Gwamna zai taba ba har da iyalinsa da kuma al’ummar Kano”.

Leave A Reply

Your email address will not be published.