Real Madrid Da Neymar Sun Kulla Wata Yarjejeniya

164

Rahotanni daga kasar Brazil sun bayyana cewa ana tunanin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dad an wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German, Neymar jr sun kulla wata yarjejeniya wadda za tasa dan wasan yakoma kasar Spaniya nan da shekaru biyu masu zuwa domin bugawa Real Madrid wasa. Real Madrid dai ta dade tana neman dan wasan tun tsohuwar kungiyarsa ta Santos dake kasar sat a haihuwa wato Brazil kafin daga baya Barcelona tayi shigar wuri ta dauke dan wasan. A kwanakin baya an bayyana cewa dan wasan yana takun saka da wasu daga cikin yan wasan kungiyar ciki hard a dan wasan gaba na kungiyar, Edinson Cabani da kuma mai koyar day an wasan kungiyar, Unai Emery. Acikin wannan satinne shugaban gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Florentino Perez ya bayyana cewa idan har dan wasan yanason ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya to dole yana bukatar ya buga wasa a Real Madrid domin acewarsa kungiyar ce kadai za ta iya bashi wannan damar. An bayyana Neymar a matsayin dan wasan da yake da burin zama shahararren dan kwallo a duniya wanda wannan buri nasa yana daya daga cikin dalilan dayasa yabar Barcelona domin kamar yadda masana harkokin wasanni suka bayyana idan har Messi yana kungiyar Neymar din bazai lashe komai ba. Kungiyoyin Manchester United da Manchester City suma suna zawarcin dan wasan wanda kwantaraginsa bazai kare ba a PSG sai a shekara ta 2022.

Leave A Reply

Your email address will not be published.