Rashin Tsorone yasa nafito Dan Boko Haram– Zayad a Shirin Dadin kowa

1,398

Mustapha Hamid

DUK wanda ya ke kalon was an kwaikwayon nan mai farin jinni na ‘Dadin Kowa’ ya san mutumin da ake kira Zayyad, wanda ya kware wajen shirya ta’addanci. To, Zayyad ba wani ba ne sai Mustapha Hamid wanda har ila yau ake kira da Mista Indiya. Matashin jarumi ne da ya kasance mara tsoro. Hakan ne ma ya ba shi damar rawa hawa rol din Zayyad domin kuwa a lokacin da a fara shirin na tashar talbijin ta Arewa24 duk wani jarumi da aka ce za a ba shi rol din sai ya ce ya na jin tsoro, amma shi ya karBa ya rika fitowa a rol din. Kuma wani abin mamaki sai rol din ya dace da shi.

Domin jin ko wanene Mustapha Hamid da kuma yadda aka yi ya samu shiga ‘Dadin Kowa’, wakilin mu a Kano, MUKHTAR YAKUBU, ya tattauna da shi.

FIM: Da farko za mu so ka gabatar da kan ka ga masu karatun mu.

MUSTAPHA HAMID: To, assalamu alaikum. Ni dai suna na Mustapha Hamid, wanda aka fi sani da Mista Indiya. Kuma tarihin rayuwa ta ni dan asalin Jihar Bauchi ne. Na yi rayuwar karatu na na firamare da sakandire a garin Zariya. Sannan kuma na yi karatu na na gaba da sakandire a garin Kano wanda kuma a yanzu a nan na ke ci gaba da zama. Kuma an haife ni a ranar 12 ga watan Fabrairu, 1984. A halin yanzu ina da mata daya da yaro daya.

Da yawa mutane su na kiran ka da suna Mista Indiya. Yaya aka yi ka samu wannan suna?

To, sunan Mista Indiya ya samu ne tun lokacin yarinta, da ya ke mahaifiya ta ta na da alaka da kasar Indiya. To, idan aka saka mana fim din ‘Mister India’ mu na kallo, sai ya zamana agogon da ya ke hannun Mista India ya na burge ni, don haka duk lokacin da za ta je kasar Indiya wajen iyayen ta sai na ce idan ta je ni tsarabar da za ta kawo min irin wannan agogon na Mista Indiya. To da haka dai na samu wannan suna, kuma har na taso da shi zuwa yanzu.

Ya aka yi ka shigo Kannywood?

Na samu kai na ne a wannan masana’anta a 1999. Ko da yake tun a wancan shekarun na ke, amma har yanzu ba a san da zama na ba. To da man ita harka haka ta ke. Kuma a lokacin ina sakandire, lokacin da aka zo za a yi wani fim aka nemi wadanda za su fito a cikin fim din kasancewar fim din ya na kunshe ne da daruruwan mutane, su kuma masu fim din ba za su iya biyan kowa kudin sallama ba, sai ya zamana ana neman wadanda za su bada gudunmawa. Kuma ni sai na ji ina da ra’ayi, kawai sai na shiga na je aka yi fim din da ni. Wannan fim din kuma sunan sa ‘Shahidin Karbala’.

A tsawon lokacin da ka yi, ko za ka iya tuna yawan finafinan da ka yi?

To, da yake lokacin da aka yi fim na farko ina rayuwar karatu ne, to ka ga ban dauki fim a matsayin sana’a ba, kuma a lokacin su daraktocin da yake ’yan Kannywood ne, sun yi sha’awar cewar su na da bukatar na ci gaba da fim, amma sai ya zama karatu ne a gaba na. Don haka ba zai yiwu ba. Saboda haka na kan yi shekara daya ko biyu ban fito a fim ba, don haka ban da na farko finafinan da zan iya tunawa na yi su ne ‘Arba’, ‘Shahid’, ‘Babbar Mace’, to da dai sauran wadanda a yanzu ba zan ya tunawa da su ba.

Da yake harkar fim din ta na da fadi, ko ka yi wata harkar bayan aktin a cikin masana’antar?

E, bayan aktin na yi wasu abubuwa wadanda ma ba a cikin industiri din ba wadanda su na da alaka da ita, domin na yi aikin jarida, inda na zama wakili kuma marubuci a wata jarida kuma a cikin industiri. Kamar maigida na Adam M. Adam, lokacin da na zo Kano mu ka hadu da shi sai kawai ya ce shi abin da ya ke bukata na zama mai aiki a bayan kyamara duk da cewar a lokacin ba ni da ra’ayin hakan, amma duk lokacin da aka ba shi aikin fim a matsayin darakta sai ya ba ni mataimakin sa.

To an san ka a shirin ‘Dadin Kowa’ da ka ke fitowa a matsayin Zayyad. Ko yaya ka yi ka samu kan ka a cikin shirin?

Shi ‘Dadin Kowa’ tambayar za ta iya kasancewa a matsayi na na darakta, ko a matsayi na na dan wasa? Idan a matsayin darakta ne, na iya cewa su tashar Arewa sun dauke ni a matsayin Mataimakin Darakta a shirin ‘Dadin Kowa’. Ko da yake lokacin da na je aiki an riga an fara shirin ‘Dadin Kowa’, an yi episodes har guda biyar, don haka mun samu za a ci gaba ne ni da wani Abdulmajid Sunusi, wanda aka fi sani da Kunle John. To, na yi ta zama a matsayin Mataimakin Darakta har zuwa lokacin da aka yi episodes 30, inda kuma daga nan aka fara ba ni matsayin Darakta har zuwa na 101. Sai kuma aka sauya min wajen aiki.

To shi kuma abin da ya shafi aktin, shi wani lokaci ne da aka yi casting din likita, lokacin da mu ka je za mu yi shutin shi da man a cikin asibitin sa ne mu ke yin sinasinan asibiti, sai mu ka ce shi ne zai fito mana a matsayin likita. Har ya amince, amma da mu ka je da yake gidan sa ya na hade da asibitin, da mu ka sanar da shi lokaci ya yi ya zo za mu fara, sai kawai matar sa ta fashe da kuka, wai ita ba ta yarda mijin ta ya fita a cikin fim ba! To, shi kuma ganin haka sai ya janye. Wannan ya sa mu ka zamo ba mu da wani zaBi na wanene zai fito a likita.

To, da yake fita daya ne, sai na ce ni kawai zan fito. Duk da yake wanda ya ke matsayin Mataimakin Daraktan a lokacin, Salisu T. Balarabe, ya dan nuna rashin yardar sa, amma daga baya da ya zama babu yadda za a yi sai na hau rol din. Amma shi ma na yi ne ba da niyyar zan ci gaba da fitowa ba.

To, ana tafiya, da aka fara zuwa rikici a fim din, an fara taBo batutuwan Boko Haram, sai ya zamana su jaruman da ake so su hau rol din Boko Haram, sai ya zamana su na jin tsoro. Kowa idan aka ce ya hau sai ya ki yarda. To, sai aka rasa yaya za a yi. To kawai sai na ce a ba ni rol din, babu wanda na ke jin tsoro. Don haka na ce tunda na taBa fitowa a matsayin likita, su gina min labarin a kan sa. Don haka sai su ka tsara ni likita ne, ina da ilima na na aikin likita da kuma na kimiyya, amma na fake da aikin asibiti ne ina aikata ta’addanci. Sai ya zama a cikin shirin ne ma na ke haduwa da ’yan Boko Haram yadda za su kai hari. To da haka dai na zama Zayyad a ‘Dadin Kowa’.

Yadda ka ke fitowa a matsayin Zayyad a ‘Dadin Kowa’, ya za ka kwatanta kan ka da yadda ka ke Mustapha ko Mista Indiya a waje?

To, Zayyad a ‘Dadin Kowa’ ya zo ya danne sunan Mista Indiya a waje. Saboda yanzu duk inda na hadu da mutane kawai Zayyad su ke kallo, ba Mista Indiya ba. Don haka yanzu kawai mutane su na kallo na a Zayyad ne.

Bayan fitowar ka a ‘Dadin Kowa’ yaya mu’amalar ka da mutane ta ke kasancewa?

To, dole ka san su masu kallo a ko yaushe su na sha’awar jarumi, musamman ma idan jarumin ya na fitowa a rol mai hadari. Don haka babu wani abu da na ke fuskanta a wajen mutane sai kauna. Saboda a iya tsawon shekarun da na yi a cikin harkar fim har zuwa 2014 da na fara fitowa a ‘Dadin Kowa’, ban fito a wani fim da ya sa na samu karBuwa, mutane su ka san ni, kamar shirin ‘Dadin Kowa’ ba. Duk da cewa na dauka mutane za su tsane ni saboda rol din, amma sai na ga su na nuna min kauna. Kuma ni ban taBa sa wa kai na burin na kambama kai na ko na wuce gona da iri a rol din don na ja hankalin mutane ba. Kawai dai ina yin rol din ne yadda ya ke; don a sauran finafinai na kan yi hakan don a san ni, amma na ‘Dadin Kowa’ ba na yin haka. Amma sai ya zama na fi samun karBuwa.

Yanayin rol din da ka ke takawa bai sa ko da a wani lokaci idan ka na yawo wasu idan su ka hadu da kai su tsorata ba?

To ba dai a guduwa, sai dai na kan zama abin tsokana, kamar lokacin da aka sauya min Bangaren aiki. Idan na fita zan yi aikin hada rahoto sai ka ji yara sun zo sun taru su na cewa, “Ga dan Boko Haram din nan na ‘Dadin Kowa’!” Sai ya zama na zama abin tsokana a wajen yara. Amma dai ni wannan ba ya wani damu na saboda yanzu kan mutane ya waye; don ka fito a wani rol ba ya na nufin kai din ne ba.

Ya ka ke ganin yadda harkar fim ta ke isar da sako?

To, ita da man harkar fim manufar kafa ta kenan tun asali. Kuma ka ga shirin ‘Dadin Kowa’ an yi shi ne don samar da hanyar da mutane za su kauce wa ayyukan ta’addanci da kuma yadda za su taimaki kan su wajen tallafa wa jami’an tsaro da bayanai da kuma abubuwa daban na taimakekeniya a rayuwar jama’a. Kuma ka ga sakon ya na isa ga jama’ar da ake yi domin su.

A karshe, wane sako ka ke da shi?

Sako na na karshe, mutane su kara wayewa da abubuwan da su ke zuwa sababbi, domin akwai masu amfani a cikin su da kuma marasa amfani, musamman ga matasa. Don haka sai su rinka lura da duk abin da za a zo musu da shi, su sa ilimi da basira wajen yin mu’amala da shi. Kuma daga karshe ina yi wa masoya masu kallon mu fatan alheri. Na gode da irin kaunar da su ke nuna mana.

Comments are closed.