Rahama Sadau Ta Zama Jarumar Kannywood Ta Farko Da Ta Samu Yawan Mabiya Miliyan 1 a Instagram

188

Fitacciyar jarumar Kannywoood da Nollywood, Rahama Sadau ta yi murnar samun yawan masoya har miliyan daya a shafin sada zumunta na Instagram.

Jarumar ta kai wannan mataki ne a wannan makon.

Sadau dai itace jaruma ta farko a Kannywood da ta kai yawan mabiya har miliyan daya.

Jaruma Hadiza Gabon ita ke bi mata baya da yawan mabiya sama da 800,000 sai kuma jaruma Nafeesat Abdullahi da ke da yawan mabiya har 700,000.

Tuni dai Sadau ta yi wa masoyanta godiya a wani sako da ta wallafa a shafin tare da jinjina masu.

Jarumar wacce kuma ‘yar kasuwa ce da ke da nata jadawalin kayan kwalliya ta shigo harkar ne daga baya-baya amma a halin yanzu ta ratsa masa’antocin shirya fina-finai na Arewaci da na kudancin kasar nan.

Comments are closed.