Rahama Sadau Ta Yi Karin Haske Game Da Gayyatar Da Akon Ya Mata Zuwa Kasar Amurka

184

Da ake hira da ita a shirin nan mai suna Kundin Kannywood na jiya Talata, wanda Aminu Sharif Momoh ke jagoranta, shahararriyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta yi karin haske game da gayyatar da ta samu zuwa kasar Amurka.

Idan mai karatu bai manta ba, shahararren mawakin nan mai suna Aliane Damala Bouga wanda aka fi sani da suna Akon shi ya gayyaci Sadau domin ta yi aiki da shi.

Toh sai dai tafiyar ta haifar da cecekuce iri daban daban daga wadanda basu fahimci lamarin ba.

Sadau ta ce ta yi matukar mamaki a lokacin da ta samu gayyata daga mawakin saboda ta san shi kuma ta dade da sanin wake-wakenshi. Ta ce ta ga wannan gayyata a matsayin wata babbar dama a gareta da ba za ta iya kin amsawa ba.

Game da rade-radin da wasu suka yi ta yi cewa Akon ya so ya sauya mata addininta zuwa kiristanci, Sadau ta yi watsi da wannan, inda ta ce wadanda ke wannan magana ba su san Akon ba, saboda musulmi ne shi wanda kuma ya dauki adininshi da muhimmanci.

Ta ce har sai da Akon ya bukaci ta bi shi da iyalinshi zuwa umrah, amma ba ta yarda ba saboda tsoron yadda mutane za su mayarda abun.

Ta ce kuma ce Akon fa matan shi uku ga wadanda ke rade-radin ta na son shi.

Comments are closed.