NNPC-Tagano Mai a kananan hukumomi 4 dake sokoto

87

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC, ya ce aiki ya yi nisa a yunkurin nemowa da kuma hako man fetur da iskar gas a jihar Sakkwato da ke arewacin kasar. Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar da ma na jihohi musamman na arewa ke kukan matsalar tabarbarewar tattalin arziki da karancin kudaden shiga. Yankunan da aka fara gano man a cikin jihar Sakkwato sun hada da Gada da Goronyo da Illela da Gudu da kuma Tangaza. Wannan bayanin ya fito fili ne bayan ganawar da gwamnan jihar ta Sakkwato ya yi da shugaban kamafanin na NNPC a Abuja babban birnin kasar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.