Na Yi Ta Daba Mata Adda Har Ta Mutu – Inji Wani Matashi Da Ya Kashe Kishiyar Uwarshi

344

Wata babbar kotu da ke zama a Jos, babban birnin jahar Plateau ta yankewa wani mai shekaru 24 hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan da ta kama shi da laifin kashe kishiyar uwarshi.

Mutumin mai suna Binfa Lamde ya amsa laifin nasa, inda ya ce ya kashe kishiyar uwar mai suna Kum Zwade ta hanyar sassara mata adda a yayin da ta ke barci da daddare.

Ya ce ya aikata haka ne bayan rasuwar kanwarshi wacce ta yi ta rashin lafiyar da asibiti suka kasa fahimtar me ke damunta. Ya ce da suka kaita wajen nai maganin gargajiya, ya fada masu cewa Kishiyar uwarce ta kama ta da maita kuma ya yi ta rokon ta sake ta, amma ta ki har sai da ta mutu.

Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ya rahoto cewa tun a watan Yulin 2014 ne aka gurfanar da Lamde a gaban kuliya.

Ya aikata laifin ne a ranar 10 ga watan Afrilun 2014.

@Alummata

Comments are closed.