NA YI JIMA’I A RAMADHANA, AMMA BA ZAN IYA KAFFARA BA, KO ZA TA FADI A KAINA ?

205

NA YI JIMA’I A RAMADHANA, AMMA BA ZAN IYA KAFFARA BA, KO ZA TA FADI A KAINA ?

Tambaya:
Assaalamu Alaikum…Dr.Ina da tambaya game da Hadisin manzon Allah (SAW)akan wani mutum da ya sadu da matar sa da rana cikin Ramadan,duba game da yadda Manzon Allah ya warware masa matsalar sa, to idan har an sami wani ya sadu da matar sa da Azumin kuma bazai iya azumiba,’yanta wuyaye,ciyarwar ba kuma bai sami wanda zai ba shi abin da zai ciyar ba yaya zaiyi.Allah ya saka da alkairi.

Amsa :
To dan’uwa kissar da ka fada ta zo a hadisi tabbatacce mai lamba ta : 616 a cikin Sahihil Bukhari, saidai malamai sun yi sabani akan mas’alar zuwa zantuttuka guda biyu :

1. Kaffarar ba za ta fadi akansa ba, za ta wanzu har zuwa lokacin da zai samu damar yin daya daga cikinsu, kamar yadda suke a jere a hadisin, saboda annabi s.aw. a cikin hadisin bai ce masa kaffara ta fadi akansa ba, ya yi masa shiru ne.
2. Kaffarar ta fadi akansa, saboda lokacin ya ce ba zai iyaba , Annabi s.a.w ya bar masa dabinon don ya ciyar da iyalansa.
Wasu malaman suna rinjayar da zance na karshe, saboda shi ne ya fi dacewa da zahirin hadisin .
Allah ne mafi sani

Don neman karin bayani duba : Al–minhaaj na Nawawy 3\182-183

Jamilu Zarewa
6\7\2015

Comments are closed.