Mutumin da ke kiran kansa A’isha Buhari ya gurfana a kotu

187

An gurfanar da wani mutum a gaban kotu bisa zargin sa da damfarar mutane sama da Dala milyan 20 a sassan duniya, in da yake bayyana kansa a matsayin matar shugaban Najeriya, A’isha Buhari.

Julius Anyawu Uche mai shekaru 48 a duniya, na amfani da hanyoyin sadarwa na zamani ne, in da yake kiran kansa Aisha Buhari, domin damfarar mutane.
Kotun Tarayya da ke jihar Legas ta tuhumi Uche da laifuka 10 a karkashin dokokin yaki da manyan laifukan Intanet, yayin da kotun ta bayyana ranar 18 ga watan Janairu mai zuwa domin ci gaba da shari’arsa.
Najeriya ta yi kaurin suna wajen damfarar jama’a ta yanar gizo a sassan duniya, in da masu aikata laifin ke boye sunayensu don cimma nasarar cutar al’umma.
RFIhausa.

Comments are closed.