Meyasa Siyasa Sai Anyi Kagge Ko Sharri – Direkta Illiyasu Abdulmumini Tantiri

191

KO SHARRI YA ZAMA KAMAR FARILLAR SIYASAR AREWA

ME YA SA SIYASA SAI AN YI KAGE KO SHARRI?

Daga Iliyasu Abdulmumini

Babu ruwan Allah wanene kai? Me kake yi? Daga ina ka fito? Duka za mu tashi gaban mahaliccinmu kuma za mu amsa duka abinda muka aikata a gidan duniya.

Ban yarda shugabannin kasar mu suna da gaskiya da amanar da zan fito in yiwa wani sharri ko in kaga mashi wani abu don zubar masa da mutunci ko kima don bani da ra’ayinshi kawai. Ta iya yiwuwa wanda kake so din kake karewa shine mai aikata wadancan abubuwan da kake kagawa wani.

Zance na a nan guda daya ne idan har ka amsa sunanka musulmi kuma kana alfahari da musulunci,to kuwa wajibi ne ka nuna hallaya mai kyau da tarbiyya irin ta musulunci. Babu ruwan Allah da siyasarka matukar ba ta cikin doron shari’a.

Mun san sakamakon KAGE ko SHARRI a musulunci? Kuma Allah ba zai yafe maka hakkin wani ba har sai wanin ya yafe maka ba.

Amma ni a hasashe na ba za mu taba samun abinda muke nema ba ga siyasa, idan kuwa halin talakawa ya zama mara kyau, ta ina za su samu shugabanni masu adalci da amfani a gare su? Ai daidai ruwa daidai tsaki. Halayyar ku shugabanninku.

Allah ya shirye mu ya ganar da mu gaskiya.

Comments are closed.