Maza ku ji tsoron Allah-Inji Samira Ahmad

217


Tauraruwar fina-finan Hausa, Samira Ahmad ta yi wani rubutu a shafinta na dandalin sada zumunta da ya jawo cece-kuce, Samira tace, Maza kuji tsoron Allah, zan yi rubutu na musamman a kanku amman ku dakaceni.
Wannan rubutu na Samira ya dauki hankulan mabiyanta inda da dama ciki hadda abokan aikinta irin su Mansurah Isah da Aminu Alan Waka da Rukayya Dawayya duk sun bayyana ra’ayoyinsu akan wannan magana.
Saidai da alama ra’ayoyin da aka bayyana akan maganar tata ba suwa Samira dadi ba. Dan kuwa ta fito ta kare kanta ta kuma caccaki masu sukarta.
Tace, Gargadi, ku tuna fa wannan shafinane kuma inada damar in rubuta abinda nake so kuma in kulle duk wanda zai yi amfani da kalmar zagi ko cin mutunci, Dan Allah ku kama kanku. Daga nace ku ji tsoron Allah tun ban fara bayyana abinda nake nufi da magana ta ba duk kun fita daga hayyacin ku, daga karshe dai ta shawarce su da su canja hali sannan kuma tace a dakace ta.
Muna fatan Allah yasa mu ji Alheri.

1

2

3

Comments are closed.