Matar da aka kama saboda ta ce an yi mata fyade

240

Ana samun karin fargaba kan ‘yancin fadin albarkacin baki a kasar Masar. An kama wasu ‘yan jarida da masu fafutuka da laifin yada labarun bogi, wanda hakan laifi ne a dokokin Masar.
Masu kare hakkin bil adama sun ce sabuwar dokar da aka zartar a watan Yuli dangane da kafofin sada zumunta yana kara dakile ‘yancin fadar albarkacin baki.
Gwamnati ta ce tana kokarin yakar yada jita-jita wacce ke dagule al-amuran kasar.

Comments are closed.