Mata Na Ta Kware A Wajen Kwana Da Mazan Banza – Miji Ya Fadawa Kotu

225Wani mutum mai shekaru 49, Gbenga Olomilua, ranar Laraba a wata kotun al’ada da ke Inanlende a garin Ibadan, ya bukaci a raba aurensa da ke tsakaninsa da uwargidansa, Rashidat, a kan zargin aikata zina.
A cewar kamfanin dillancin labaran Nijeirya (NAN), Olomilua, ya fadawa kotun cewa aurensa na tsawon shekaru 10 na fuskantar kalubale wadanda suka rashin kunya, da yaudara da kuma yawan kwarwa.

“Na aure ta a lokacin da ita ba kowa ba ce sanna kuma ba ta da komai. Duk da cewa ban biya sadakinta ba, na dauke nauyinta ta hanya kula da duk wani bukatarta.


“Ina aiki a birnin Legas, amma ni kan dawo gida Ibadan a kowane karshen mako. Abun takaici shine, ta kan yi amfani da damar rashin zama gida wajen koyan yawon iskanci wajen kawayenta.
“Yanzu haka ta kwarai, har ya kai lokacin da ya k nunawa. Ba kerr ta ke zama gida domin ta kula d ‘ya’yan mu.

“Tana yawan magana, sannan ba ta jin magana, ko kuma yin umurni na a matsayi na na mijinta.
“Sakamakon hakan ne, ya sa na yanke hukuncin raba auren mu da ke tsakani na da ita,” Olomilua ya ce.

NAN ta ruwaito cewa Rashidat, ‘yar shekaru 32, ta buakci kotu da ta raba auren da ke tsakaninta da ke mijinta saboda rashin kwanciyar hankali da ta ke fama da shi a gidan aure.

Matar da zargi mijinta da yi ma ta dukar tsiya a duk lokacin da suka samu matsala.
“Ya taba yanke ma ni gashin kai da reza a wani fada da mi ka taba yi. Mai shari’a, ina tsoro saboda ban san mai zan yi da gashin kai na ba.

“Bai kula da ni kamar yadda ya kamata miji ya kula da matarsa ba. Yana cin zarafi na, sannan kuma bai biya ma ni bukatu na,” ta ce
Rashidat ta ce tunda babu wani alamar soyayya a auren da ke tsakaninsu, ta bukaci kotu ta raba auren da ke tsakaninsu.

Alkalin kotun, Cif Ramoi Olafenwa, ba tare da bata lokaci ba ya raba aure da ke tsakanin ma’auratan sannan ya bada rikon dan su na farko zuwa ga Olomilua.

Duk da haka, Olafenwa ya ba Rashida rikon dan su na biyu sannan kuma ya umurci mijin da ya biya ta naira N4,000 a kowane wata don kula da yaron.

Ya kuma ba ma’auratan shawara da su kauracewa juna.

Leave A Reply

Your email address will not be published.