Masu Aikata Muggan Laifuka Da Ake Tubarwa Suna Yi Wa Gwamnati 419 Ne -ALI KWARA

103
An bayyana tubar da masu aikata manyan laifuka da gwamnati ke yi a matsayi wata babbar hanya da masu manyan laifi ke damfara gwamnati, yayin da suma wasu jami’an gwamnati ke yin amfani da wannan hanya wajen zuke dukiyar gwamnati da sunan an tallafawa masu aikata laifukan da suka tuba don su samu kudin da za su lura da kan su su daina aikata laifuka.
Shahararren mai fafutukar samar da taimako wajen inganta tsaro da tallafawa jami’an tsaro, Alhaji Ali Mohammed Kwara, shi ne ya bayyana haka cikin hirar sa da manema labarai a garin Azare da ke Jihar Bauchi. Inda ya bayyana cewa abin mamaki ne yadda a kullum masu aikata miyagun ayyuka madadin ace suna raguwa sai karuwa suke yi saboda wadanda suke ci da sunan suna samar da zaman lafiya suna da yawa.
Lamarin da ya bayyana cewa matukar ana son komai ya daidaita dole sai gwamnati ta dawo da hankalinta wajen yaki da masu ci da sunan ‘yan ta’adda an fiskanci gaskiya ta hanyar nuna ba sani ba sabo kafin komai ya daidaita a daina salwantar da rayukan bayin Allah da ba su ji ba basu gani ba.
Alhaji Ali Kwara ya ce cikin hirarsa da wakilin mu kusan shekaru goma ya sha yin hasashen idan ba an yi maganin masu ci da sunan masu aikata laifi a kotuna da ofisoshin lauyoyi da na jami’an tsaro ba, to za a wayi gari masu aikata laifuka za su nemi fin karfin hukuma.
Wannan hasashe ya kasance a daidai wannan lokaci inda Ali Kwara ya bayyana cewa lamarin a fili yake ga dukkan mai hankali idan ya yi karatun baya ta hanyar lura da irin gudummowar da wasu mutane ke bayarwa wajen kubutar da masu laifi a kotuna ko ofisoshin hukumomin tsaro a shekarun baya, yace lamarin ya sa wasu mutane kalilan da ke cikin wadancan gwamnatoci suka arzuta don haka wannan abu ya ci gaba da samun gurbi ana damfarar gwamnati saboda masu aikata laifin sun sani ko an kai su gaban hukuma akwai wadanda ke daukar kwangilar tsara lauyoyi da tuntubar manya har sai mutum ya kubuta daga fuskantar hukunci.
Daga baya kuma mai laifi ya koma ruwa ya nemi kudi ya biya irin wadannan mutane ladan da suka yi.
Yace idan irin haka ta auku wadanda aka yi wa laifi suka kai kara bayan watanni suka ga wanda ya kwashe musu dukiya ko ya kasha musu dan uwa a waje yakan zamanto suma irin wadannan mutane su kudiri aniyar daukar fansa daga nan kuma sai suma su zamo ‘yan ta’adda inda sukan ci gaba da yin abin da suke so tare da cin zarafin mutane da haka masu aikata laifi a kasar nan suka kara yawa, saboda ganin ko sun shiga hannun hukuma akwai wadanda ke daukar kwangilar shirya lauyoyin da za su kubutar da su daga fuskantar hukunci, don haka har an kai wani matsayi da basa tsoron hukunci ko gwamnati.
Alhaji Ali Mohammed Kwara yace ya jima da lura da yadda aka sa gaba a kasar nan kuma yana sanar da hukuma wasu gwamnoni da kwamishinonin ‘yan sanda da manyan jami’an tsaro da suka gabata sun sani ya sha fada za a fiskanci matsalar tsaro a Nijeriya musamman a arewa maso gabas da arewa maso yamma. Kuma dukkan masu binsa a kafafen watsa labarai da jaridu za su zama shaida saboda a duk lokacin da ya kama masu aikata laifi shekaru kusan goma baya za a taras suna da iyayen gida barayin zaune. Don haka yace ya sha jan hankalin gwamnatocin da suka gabata kan su rika taka tsantsan da abin da ke faruwa a kasar nan domin kullum matsala karuwa ta ke yi, uwa uba kuma aka sake dawowa rashin aikin yi ya karu tsakanin matasa inda suke neman rayuwa ta kowane hali.
Ya kara da cewa abin mamaki ne yadda wadanda ke cikin gwamnati a arewa maso yamma da wasu sassa na arewacin Nijeriya ke shirya tubar da masu aikata muggan laifuka da suka shafi kisan kai ko garkuwa da mutane da fashi da makami, a dauki wani dan kudi a basu a ce su dawo cikin jama’a alhali tsuguni bata kare ba. Amma idan an yi la’akari da yawan kudin da ake fitarwa daga aljihun gwamnatin jihar da aka shirya wannan aikin za a taras bai wuce kashi biyar ko goma cikin dari na kudin ake rabawa wadanda aka tubar ba sauran wasu jami’an gwamnati ke kwanciya a kai su arzuta kan su. Haka kuma gobe za a sake tattaro wasu masu laifi daga gidan yari ace an tubar da su an basu tallafi amma idan an kwana biyu sai a sake kama wadannan da aka tubar cikin masu aikata laifi, lamarin ya zamo damfarar 419.
Ali Kwara ya bayyana irin wannan aiki a matsayin wata babbar hanya ta damfarar gwamnati a Nijeriya don haka ya kamata shugabanni su farga su tuba su daina karbar uzurin tubar da masu laifi, madadin haka kamata ya yi su bar hukunci ya yi aiki a kansu zu zauna a gidan yari na wani tsawon lokaci don ya kasance darasi a gare su, kuma zai taimaka wajen ganin irin wadannan mutane idan sun fito daga zaman kadaici na hannun hukuma tare da samu horo ya kasance sun natsu. Amma daga inda aka ce sun aikata laifi an kubutar da su an basu kudi kwana biyu za su cinye kudin su rasa abin yi sai su koma aikata laifuka da yin barazana wa tsaron kasa da jami’an tsaro da suka taimaka wajen kamo su daga inda suka buya.
Don haka Alhaji Ali Kwara ya bayyana cewa an jima ana tubar da masu aikata laifi a jihohin Zamfara da Katsina da wasu wurare, tare kuma da daukar nauyin biyan tara ga wadanda suka aikata laifi a fito da su amma idan sun fito sukan zamo barazana ga alkalan da suka daure su ko jami’an tsaron da suka taimaka aka kama su ko wadanda suka yi wa laifin. Don haka ya roki gwamnati da majalisar tarayya ta sanya doka mai tsanani kan irin abin da ke faruwa na yafewa manyan masu laifi da nufin za su daina amma kullum abin karuwa ya ke yi.
Inda ya bayyaan cewa ko a kwanakin baya sun yi gagarumin aiki karkashin Sifeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya kuma sun kama masu laifi sosai har an kashe wasu a bata kashi yayin da suma sun illata jami’an tsaro, amma duk da kokarin da hukumar ‘yan sandan Nijeriya ke yi wajen ganin an samu saukin irin wannan matsala a kullum kotuna da lauyoyi suna sanyaya guiwar ‘yan sanda da sojojin da ke wannan aiki da kuma su da ke taimakawa gwamnati don a kawo karshen wannan matsala ta ta’addanci a Nijeriya. Don haka ya yi fatar mutane za su taimaka a duk inda suke wajen bayyana barayin zaune ga gwamnati don a samu sauki wajen magance irin wannan matsala da ta tunkaro Nijeriya game da zubar da jinin bayin Allah da ba su ci ba ba su sha ba, lamarin da ya ce sai mutane sun tashi tsaye wajen yin addu’a da taimakon hukuma da tona asirin masu aikata laifuka kafin a samu saukin lamarin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.