Manyan Mata 5 mafi shahara da farin jini a dandalin kannywood a yanzu

245

Dandalin shirya fina-finan Hausa ta Kannywood na da albarkattun kyawawa kuma kwararrun yan wasa mata da suka amsa sunansu na kyawawa. Baya ga kyawu da wadannan mata ke da shi sun kasance masu kwazon aiki.
Hakan ya sa muka yi amfani da wannan dama wajen kawo maku wasu daga cikin shahararrun jaruman da suka yi fice hade da farin jini a waje muta Ga wasu biyar daga ciinsu:

1. Halima Yusuf Atete

Manyan Mata 5 mafi shahara da farin jini a dandalin kannywood a yanzu Source: UGC An haifi Halima Yusuf wacce aka fi sani da Halima Tete a ranar 9 ga watan Disamba 1988. Jarumar ta shiga harkar fim da kafar dama inda tauraronta ke kan haskawa, ta kuma fito a fina-finai da dama. Fim din dakin Amarya ne ya fito da ita.

2. Hafsat Idris Baraniya

Manyan Mata 5 mafi shahara da farin jini a dandalin kannywood a yanzu Source: UGC Hafsat Idris wacce aka fi sani da sunan wani fim da ta fito wato ‘Barauniya’ ta kasance daya daga cikin hadaddun matan kannywood. An haife ta a garin Shagamu amma yar asalin jihar Kano ce.

3. Nafisa Abdullahi
Manyan Mata 5 mafi shahara da farin jini a dandalin kannywood a yanzu Source: UGC Nafisa ta kasance daya daga cikin kwararrun jarumai da ke da kwazon aiki. An haife ta a ranar 23 ga watan Janairu a garin Jos, Jihar Plateau. Nafisa ta kasance kyakyawa. Ta shahara a fim dinta naSai wata rana.
4. Rahama Sadau

Manyan Mata 5 mafi shahara da farin jini a dandalin kannywood a yanzu Source: Twitter An haifi Rahama Sadau a ranar 7 ga watan Disamba, 1992 a jihar Kaduna.Tana daya daga cikin shahararrun yan matan Kaannywood, wacce ta shahara tun bayan bayyanarta a wani fim mai suna “Gani ga wane”.

5. Hadiza Aliyu


Manyan Mata 5 mafi shahara da farin jini a dandalin kannywood a yanzu Source: Facebook Hadiza Aliyu wacce aka fi sani da Hadiza Gabon ta kasance daya daga cikin matan Kannywood mafi shahara, uwa uba ga kyau. An haifi Hadiza a ranar 1 ga watan Yuni 1989 a Libreville, a kasar Gabon. A kwanan ne kamfani Dangote ya nada ta a matsayin jakadiyar kamfanin.

Comments are closed.