Man City ta ragargaji tsohon golanta da cin Burnley 5-0

162

Manchester City ta sa tsohon mai tsaron ragarta Joe Hart rashin bajintar da bai taba yi ba a Etihad bayan da ta zura masa kwallo 5-0 a karawarsu da Burnley, ta kara zama ta daya a teburin Premier.
Da wannan sakamako Manchester City tana matsayi na daya bayan wasa tara da maki 23, yayin da Burnley take ta 13 da maki 9. Liverpool wadda ta bi Huddersfield gida ta ci ta 1-0 tana ta biyu da maki 23 kamar City, amma da bambancin yawan kwallo har 10 a tsakaninsu.
Da farko mai tsaron ragar Burnley kuma tsohon golan Manchester City din Joe hart, wanda a wannan karon ya dawo filin na Etihad bayan ya kawo karshen zamansa na shekara 12 a bazara, ya nemi hana tsohuwar kungiyar tasa katabus na samun maki ukun.
Hart wanda yake da farin jini a wurin magoya bayan City a lokacin yana kungiyar, ya yi kokari sosai a kashin farko na wasan ya hana Sergio Aguero da David Silva daga ragarsa, amma kuma sai ya rasa wannan karsashi wajen dakatar da Agueron a wani ba-ni-in-ba-ka da ‘yan wasan biyu suka yi a minti na 17.
Abubuwa sun tabarbarewa Hart da Burnley din bayan da aka shiga kashi na biyu na wasan inda Bernardo Silva ya ci ta biyu a minti na 54, kafin minti biyu tsakani Fernandinho ya kara ta uku.
Wasa ya nutsa a minti na 83 Mahrez ya jefa ta hudu sannan da cikar minti na 90 kuma Sané ya ci cikammaki, ta biyar.
Hart mai shekara 31 zai so a ce ba a daga ragarsa ba a wasan kamar yadda ya yi suna da hakan a lokacin yana City, domin ya yi wasa 82 a gida wadanda ba a zura masa kwallo a raga ba.
To amma maimakon hakan a wannan wasa nasa na 180 a filin na Etihad, kuma na farko a matsayin abokin karawa, an daga ragarsa sau biyar a karon farko.

Sakamakon sauran wasannin Premier na Asabar
Bournemouth 0-0 Southampton
Cardiff City 4-0 Fulham
Newcastle United 0-1 Brighton
WEst Ham United 0-1 Tottenham
Wolverhampton Wandarers 0-2 Watford

Leave A Reply

Your email address will not be published.