Malaman makarantar firamare 2 sun yi ma daliban su fyade a jihar Bauchi

8,105


A ranan alhamis rundunar ‘yan sandar Jihar Bauchi ta gurfanar da wasu malaman makarantan firamare da ke Unguwan Dutsen Tashi dake garin Bauchi a gaban kotu bisa zargin aikata laifin fyade ga wata daliban su.
Malaman makarantar firamare 2 sun yi ma daliban su fyade a jihar Bauchi Kwamishinan yan sandar Jihar Garba Baba Umar, yace wadanda ake zargin sun lallabi yarinyar ne zuwa wani wuri in da suka aikata fyaden a kanta.
Kamar yadda Ahmadu Bauchi ya sanar mana, Malaman makarantan dan Shekara talatin da tara ne 39 da kuma dan Shekara talatin da uku 33, ” Kwamishinan ya nuna takaicin sa akan hakan musamman ganin ya auku ne tsakanin malamai da daliban su. Yace ‘yan sanda a jihar ba za suyi kasa-kasa ba wajen hukunta duk wanda aka kama yana aikata irin wannan aiki.
@Naij

1 Comment
  1. Ibrahim Magaji says

Comments are closed.